✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga da ’yan daba suna ci gaba da addabar Amurka da Ingila

Ko a ranar Lahadin da ta gabata sai da suka kashe mutum biyar a Amurka

  • Sun kashe mutum biyar ranar Lahadi

’Yan bindiga da ’yan daba suna ci gaba da addabar kasashen Amurka da Ingila inda a ranar Lahadin da ta gabata suka kashe mutum biyar a hare-hare dabandaban da suka kai.

Rahotanni sun ce wani dan bindiga ya harbi mutum biyar a harabar Jami’ar Virginia a yammacin Lahadin da ta gabata inda mutum uku suka rasu biyu kuma suka samu miyagun raunuka, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.

’Yan sandan da suke jami’ar sun fadi a sakon Twitter cewa an kama dan bindigar wanda daga farko ya tsere ‘dauke da miyagun makamai.’

’Yan sandan suna zargin wani dalibi mai suna Christopher Darnell Jones da aikata ta’asar, kuma sun ce tuni hukumomin tsaro suka kama shi.

Sun ce Jones ya aikata wannan ta’asa ce sanye da “jaket ja da wandon jins mai ruwan algashi da jan takalmi” kuma ya je ne a cikin wata bakar motar alfarma da lambar birginia TWd3580.

Wani sakon imel da mataimakin shugaban jami’ar ya tura wa kungiyar dalibai ta bukaci su rika taka-tsantsan tare da kiyaye dokokin kariya da aka sa a makarantar ganin yadda hare-haren suke ci gaba.

Wannan harbi shi ne na baya-bayan nan da kwalejoji da manyan makarantun Amurka ke fuskanta a ’yan shekarun nan.

Zubar da jinin ya jawo muhawarar a takaita mallakar bindiga a Amurka.

A Ingila kuma mutum biyu aka kashe yayin da na uku yake kwance a asibiti rai-kwakwaimutu-kwakwai, bayan da wani dan daba ya daba musu wuka a garin Bedfordshire.

Tuni hukumomi suka kaddamar da bincike bayan da aka gano gawarwakin matasa biyu da aka raunata da wuka a garin yayin da na uku ke jinya.

Jami’an agajin gaggawa sun gano mutum uku da aka daba wa wuka—kuma biyu sun mutu a wurin, inda aka dauki na uku zuwa asibiti inda yake cikin matsanancin hali.

An kai dimbin ’yan sanda yankin inda suke ci gaba da bincike, kuma babban Sufurtandan Binciken, Carl Foster ya ce: “Wannan abu ne mai daga hankali da ya jawo mutuwar matasa biyu kuma na uku ke kwance rai-kwakwaimutu-kwakwai.

“Ina sane da damuwar da mutanen yankin suke ciki, amma daga abin da na fahimta za mu magance matsalar ba za ta ci gaba da zama barazana ga jama’a ba.

“Babu wani dalilin yin wannan ta’asa kuma za mu yi duk abin da za mu iya don kamo masu hannu a ciki.

Yankin na cike da jama’a a yanzu kuma ina kira ga jama’a duk wanda ya ga yadda abin ya faru, ko wani abu da zai kai ga gano haka, ya tuntubi ’yan sanda,” in ji shi.