✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun bukaci man fetur da sigari a matsayin fansar basaraken da suka sace a Kaduna

’Yan bindigar sun sace Dagacin ne tare da wasu manoma a Kurmi, kusa da Chikwale a yankin na Kachia.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Ayuba Dodo Dakolo, Dagacin kauyen Rijana da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun sace Dagacin ne tare da wasu manoma a Kurmi, kusa da Chikwale a yankin na Kachia.

Wasu majiyoyi daga Rijana sun shaida wa Aminiya cewa daga cikin ababen da ’yan bindigar suka bukata har da man fetur da sigari a matsayin fansar basaraken da suka sace.

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai daga kiran wayarsa ba ballantana a samu tabbacin rahoton a hukumance.

Amma wani babban jami’i ya shaida wa manema labarai cewa jami’an tsaro sun samu masaniya kan faruwar lamarin.

Kauyen Rijana dai na nan akan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da mutane ke yawan bi, kuma hanyar ta yi kaurin suna saboda yawan hare-haren ’yan bindiga, wadanda ke tare matafiya su yi garkuwa da su.