✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun far wa hanyar Kaduna zuwa Zariya

'Yan sanda sun tarwatsa 'yan bindiga 40 da suka tare hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta dakile wani dan bindiga daga yin garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Zariya ranar Lahadi.

Rundunar ta ce matafiya biyu sun samu rauni sakamakon harbin bindiga, kuma suna asibiti suna samun kulawa.

Kakakin rundunar, Mohammed Jalige ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ta tarwatsa wasu ’yan bindida 40 da suka tare haryar Kaduna zuwa Zariya a ranar Lahadi.

Jalige ya ce babu wanda aka yi garkuwa da shi ko ya samu rauni a yayin farmakin, sai dai dan bindigar da aka kama wanda ke Asibitin Kwararru na Barau Dikko, inda yake murmurewa.

Hanyar Kaduna dai ta zamo wani waje da ’yan bindiga ke addabar mutane, inda da dama suka kaurace mata saboda karancin tsaro a kanta.