✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun hallaka mutum 10 a Sakkwato

Sai da aka yi artabu da ’yan banga kafin ’yan bindigar suka kutsa cikin kauyen

Akalla mutum 10 sun rasu bayan ’yan bindiga sun kai hari a kauyen Rabah da ke Jibar Sakkwato.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta tabbatar da rasuwar mutanen da wasu mutum biyu da suka jikkata a harin da aka kai da tsakar ranar Talata.

Kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Sanusi Abubakar, ya ce sai da ’yan bindigar suka yi artabu da ’yan banga kafin suka samu shiga cikin kauyen suna harbia a kan mai uwa da wabi.

A cewarsa, ’yan bindigar sun kuma yi awon gada da dabbobi masu yawa da ba akai ga tantance adadinsu ba.

Wani mazaunin garin, Jamilu Sani Rabah ya ce mutum 11 ne aka kashe, yayin da wasu da dama kuma suka bace.

Ya koka bisa rashin ganin wakilan gwamnati a wurin jana’izar mutanen da aka kashe din.

“Ko ba komai ya kama a turo wakilci, idan har shi gwamna ba zai iya zuwa kauye domin yin ta’aziyya ba,” inji shi.