✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai wa tsohon Gwamnan CBN, Soludo hari

Sun bindige ’yan sandan da ke tsaronsa a lokacin wani taro

Tsohon Gwaman Babban Bankin Najeriya (CBN) Charles Soludo ya tsallake rijiya da baya a hannun ’yan bindiga.

’Yan bindigar sun bude wuta tare da kashe uku daga cikin jami’an ’yan sandan da ke tsaron Soludo a lokacin da yake yin taro da matasan mahaifarsa ta Isuofia a Jihar Anambra a ranar Laraba da dare, lamarin da ya sa mahalarta taron suka ce kafa me na ci ban ba ki ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Anambra, DSP Ikenganya Tochukwu, ya ce jami’an Rundunar sun kama mutum daya da take zargi da hannu a harin.

Tsohon Gwamnan CBN din dan takarar gwamnan Jihar ne a zaben da ke tafe ranar 6 ga Nuwamba, 2021, a karkashin inuwar jam’iyyar APGA, in the November 6, governorship election.

Sakataren gamayyar kungiyoyi masu goyon bayan Soludo (YEES), Dokta Nelson Obinna Omenugha, ya tabbatar da kashe harin da cewa, “tabbas an kai hari a Afuzo da ke Isuofia a Karamar Hukumar Aguata, Jihar Anambra.”

Ya kara da cewa mharan sun kuma yi awon gaba da Kwamishina Kula da Kyautata Rayuwar Al’umma, Emeka Ezenwanne, sannan ya yi ta’aziyya ga iyalan mamatan.

Majiyoyi sun kma tabbatar cewa Soludo na nan cikin koshin lafiya bayan harin.