✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe jami’an ’yan sanda 13 a Zamfara

Maharan sun tsere yayin da sojojin da ke garin suka ci karfinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindiga sun kashe jami’an ’yan sanda 13 da wasu fararen hula uku a Jihar Zamfara.

Hakan ta faru ne ranar Lahadi yayin wani hari da suka kai wa sansanin ’yan sandan da ke Kurar Mota a Karamar Hukumar Bungudu.

Tun da farko dai maharan suka yi yunkurin kai hari Magami, wani gari da ke da tazarar kilomita Kudu da Gusau, babban birnin jihar, amma sojojin da ke yankin suka fatattake su.

Wani mazaunin garin ya shaida wa wakilinmu cewa, “Maharan sun tsere yayin da sojojin da ke garin suka ci karfinsu.

“Bayan haka ne suka koma wani gari da ke tsakanin garuruwan Magami, Dankurmi da Dangulbi, inda suka kashe mutum daya sannan suka cinna wa wasu shaguna hudu wuta.

“Da suka gama da nan sai kuma suka haura garin Kurar Mota inda suka bude wuta kan wani sansanin ’yan sanda da ke kusa da Asibitin garin, inda daga nan kuma suka arce cikin jeji.

“An garzaya da jami’an ’yan sandan da suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa birnin Gusau a cikin wani ayari na motocin ’yan sanda, a cewar mazaunin mai suna Kabiru Dansada.

Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ya sha alwashin waiwayar wakilinmu domin tabbatar masa da ingancin rahoton.