✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe lauya da matarsa a Binuwai

‘Yan bindigar sun kasha matar lauyan mai suna Barrister Moses Udam, har cikin gida da misalin karfe 11:30 na dare.

A daren ranar Talata ne wasu ’yan bindiga suka kashe wani lauya  da matarsa da wani bako a yankin Agbo dake Makurdi babban birnin jihar Binuwai.

’Yan bindigar sun kashe matar lauyan mai suna Barista Moses Udam, har cikin gida da misalin karfe 11:30 na dare tare da raunata wani mutum daya.

Aminiya ta gano cewa mamacin ya yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa a ranar, kafin daga bisani ’yan bindigar su zama ajalinsa.

Rahotanni sun ce jim kadan da faruwar lamarin rundunar soji ta bayyana a wajen, kafin zuwan jami’an ‘yan sanda wanda daga nan suka kwashe gawarwakin zuwa asibiti.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan jihar DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Catherine ta ce harin ’yan bindigar ya yi sanadin rasa rayukan mutum biyu, guda kuma na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar (BSUTH), inda yake ci gaba da murmurewa.