✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 4 a Bauchi

An kuma gano wata ma'ajiyar makamai da ake zargin ta 'yan bindiga ce a jihar.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, ta tabbatar da kisan mutum hudu da wasu ‘yan bindiga suka yi a kauyen Gambar Sabon-Layi da ke Karamar Hukumar Tafawa Balewa a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmad Wakil ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Bauchi a ranar Lahadi.

Ya ce ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da tsakar daren ranar Asabar, inda kuma suka yi awon gaba da wani mutum guda daya.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aminu Alhassan, ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin damke wadanda suka kai harin.

“Rundunar ta samu kiran gaggawa ne a ranar 22 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 3:45 na dare.

“An sanar da mu cewa a wannan ranar da misalin karfe 2:00 na dare wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Gambar Sabon-Layi inda suka far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

“Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun shirya zuwa wurin da lamarin ya faru karkashin jagorancin DPO na yankin Tafawa Balewa.

“Bayan zuwan jami’anmu wurin da lamarin ya faru, an kwashe wadanda abin ya shafa zuwa Babban Asibitin Tafawa Balewa domin kula da lafiyarsu,” in ji shi.

A halin da ake ciki kuma, jami’an rundunar ‘yan sandan da ke aiki da bayanan sirri, sun gano wata ma’ajiyar makamai da ake zargin ta masu garkuwa mutane ce a unguwar Tudun Wada da ke Liman Katagum a Karamar Hukumar Bauchi.

Wakil ya ce ‘yan sanda sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku da karamar bindiga guda daya, alburusai, kakin sojoji guda daya, da kuma wanduna guda biyu na ‘yan sanda.