✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe shugaban karamar hukuma a Jihar Taraba

’Yan bindigar sun hallaka mutanen ne bayan da suka fahimci ana biye da su.

Wasu ’yan bindiga a sun kai hari a jihar Taraba inda suka kashe shugaban karamar hukumar Ardo-Kola da dan uwansa.

Tun da farko dai an sace Shugaban Karamar Hukumar mai suna Salihu Dovo da dan uwansa Timothy Aminu a gidansa dake anguwar Sabon Gari a Jalingo da misalin karfe daya na daren ranar Talata.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun hallaka mutanen ne bayan da suka fahimci ‘yan sanda da yan banga na biye da su.

Daga nan ne sai suka harbe shugaban karamar hukumar da dan uwan nasa kuma suka bar gawarwakinsu a wani kauye mai suna Nahuta dake hayin Kogin Lamurde.

Kakakin Rundunar ’yan sandan Jihar Taraba, DSP David Misal ya tabbatar da aukuwan lamarin inda ya ce tuni suka kama mutane uku wadanda ake zargi da hannu a sacewa da kashe shugaban karamar hukumar ta Ardo-Kola.

DSP Misal ya ce kuma ce tuni rundunar ta fara gudanar da bincike domin zakulo wadanda ke da hannu a wannan aka-aikar.