✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe soja 2, sun saki fursunoni a kurkukun Kogi

Rahotanni sun ce maharan sun kuma saki fursunoni da dama.

’Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a wani hari da suka kai gidan kurkukun garin Kabba da ke Jihar Kogi.

Rahotanni sun ce maharan sun kutsa kai gidan yarin ne da sanyin safiyar ranar Litinin sannan suka saki fursunoni da dama.

An dai kashe sojojin ne a wani shinge da suka kafa dab da gidan yarin wanda ke kan babbar hanyar Lakwaja zuwa Okebukun zuwa Kabba a Jihar.

Kazalika, wasu masu gadin gidan yarin suma sun sami raunuka sakamakon harin.

Sai dai wasu majiyoyi daga gidan yarin sun ce an sake kama wasu daga cikin fursunonin da suka arce.

Da yake tabbatar da harin, Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda mai kula da shiyya ta takwas da ke Jihar, Ayuba Edeh ya ce yanzu haka suna nan suna kokarin ganin sun cafko maharan.