✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

’Yan bindiga sun kashe ‘Yan sa-kai 30 a Zamfara

Maharan sun sace shanu da dama.

Wasu ’yan bindiga sun kashe akalla ‘yan sa-kai 30 a yankin Gidan Dan Inna da ke gundumar Auki ta Karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce maharan sun farmaki yankin na Gidan Dan Inna inda suka sace shanu da dama.

Kazalika, bayanai sun ce maharan sun kashe wasu daga cikin mazauna yankin sannan suka kada shanunsu zuwa daji.

Wani manomi mai suna Umar Kadowa da ya hangi yadda lamarin ya kasance ya shaida cewar, maharan sun fahimci wasu ‘yan banga na bin bayansu, wanda hakan ne ya sa suka rabu gida biyu.

“Wasu daga cikinsu sun kada shanun zuwa daji yayin da ragowar suka tsaya suka farmaki ’yan bangar da suka bi sahunsu da nufin kwato shanun da suka sace.”

Manomin ya ce maharan sun yi wa ‘yan sa-kan kofar-rago inda suka bude musu wuta, kuma suka samu nasarar kashe akalla mutum 30 daga cikinsu.

A cewarsa tuni aka mika gawarwakin wadanda aka kashe zuwa kauyukansu don yi musu sutura.

Sai dai neman jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya ci tura, saboda wayarsa ba ta shiga.