✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Ministoci 7 za su ziyarci birnin Madrid

Wannan dai ita ce ziyara irinta ta farko da Shugaban Najeriyar zai kai Spain.

Fadar Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci birnin Madrid na kasar Andalus wato Spain, domin gana wa da Firaiminista Pedro Sanchez.

Balaguron wanda zai wakana a ranar Talata, 31 ga watan Mayun 2022, na dauke ne cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Femi Adesina ya fitar.

Mista Adesina ya ce Firaiminista Pedro Sanchez din ne ya gayyaci mai gidansa inda za su tattauna tare da rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da kuma fahimtar juna kan batutuwa da dama da suka shafi ci gaba da inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

A cewar Adesina, batutuwan sun hada da: musayar wadanda aka kama kan zargin aikata laifi, al’amuran al’adu, hadin gwiwa wajen yaki da laifuka da inganta tsaro, da kuma batutuwan da suka shafi wadanda suka dogara da ma’aikatan da ke kula da harkokin diflomasiyya.

Ya ce sauran batutuwan da ke cikin ajandar shugaban kasar sun hada da hadin gwiwa a fannin makamashi, kasuwanci da zuba jari, sufuri, kiwon lafiyar jama’a da raya wasanni.

Adesina ya ce a wata ganawa ta daban yayin ziyarar wadda ita ce irinta ta farko da Shugaban Najeriyar zai kai, zai kuma gana da Shugaban Spain, Mai martaba Sarki Felipe VI.

Kazalika, Adesina ya ce tawagar Shugaba Buhari za ta kunshi akalla ministoci bakwai da za su masa rakiya da suka hada da; Ministan Harkokin Ketare, Geoffrey Onyeama; Atoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN); Ministan Masana’antu, Cinikayya da Zuba Jari, Otunba Adeniyi Adebayo; Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed; Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola; Ministan Matasa da Raya Wasanni, Sunday Dare; da Karamin Ministan Lafiya, Olorunnimbe Mamora.

Sauran ’yan tawagar sun hada da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (rtd); Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da kuma Shugabar Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa.