✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun mamaye asibiti suna neman likitoci

Sun yi awon gaba da wata nas da wata mai kula da mara lafiya.

’Yan bindiga sun mamaye Babban Asibitin Dansadau suna neman likitoci su je su kula da ’yan uwansu da aka ji wa rauni a cikin daji.

A mamayar ta Babban Asibitin da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar, maharan sun dauke ma’aikaciyar jinya da wata mai jinyar mara lafiya.

Mazauna garin sun ce bayan ’yan bindigar sun kai wani hari da misalin karfe 1 na dare ne suka kutsa kai tsaye zuwa sashen kula da marasa lafiya na asibitin suna neman likita ko nas-nas.

“Da ba su samu kowa a wurin ba sai suka yi ta shiga dakunan marasa lafiya, suka sace wata nas da wata mai kula da mara lafiya.

“Sun kuma shiga gidajen ma’aikata suna neman likitoci da ma’aikatan jinya amma ba su samu kowa ba,” inji majiyarmu.

Sun kwashi kashinsu a hannu

’Yan ta’addan dauke da makamai sun yi yunkurin kai hari ne a garin Maigoge, mai nisan kilomita shida arewa da garin Dansadau.

“Sun yi wa garin kawanya amma ’yan banga sun kare shi sosai suka kuma kashe wasu ’yan bindiga tare da jikkata wasu da dama.

“Sun mamaye asibitin ne don sace ma’aikatan jinya da likitoci saboda su yi jinyar ’yan uwansu da suka ji rauni a cikin daji.

“Maigoge yana daya daga cikin ’yan tsirarun al’ummomin Masarautar Dansadau da aka sani suna kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga,” inji mazaunin garin.

Ya kara da cewa yanzu “Ma’aikatan cibiyar lafiyar ba sa aikin dare, suna zuwa ne kawai su duba marassa lafiya da rana, daga nan sai su shiga cikin gari su kwana, galibi a wuraren da ba a bayyana ba,” inji majiyar.

A halin da ake ciki, Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya, Reshen Jihar Zamfara, Dakta Mannir Bature wanda ya tabbatar wa wakilinmu harin ya ce kungiyar ta damu da abin da ya faru, ya kara da cewa za su gudanar da taron gaggawa a jihar a ranar Asabar domin tattaunawa a kan lamarin..