✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mai gari da mutum 15 a Kaduna

Maharan sun tisa keyar mai garin da wasu mutum 15 daga kauyen.

’Yan bindiga sun kashe akalla mutum daya tare da sace mutum 16 ciki har da mai gari a unguwar Kurmin Sata a Karamar Hukumar Chikun da ke  Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru da misalin karfe 12:16 na daren ranar Asabar, yayin da maharan suka yi wa garin kawanya, suka dinga harbi kan mai uwa da wabi.

Wata majiya daga jami’an tsaron hadin guiwa ta JTF ta ce “Mai gari da sauran yara da mata na daga cikin wadanda maharan suka sace; wanda ya rasu kuwa harsashi ne ya same shi lokacin yana cikin gida yayin da suke harbi,” cewar majiyar.

Majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana cewa da farko mutum 20 ’yan bindigar suka sace, kafin daga bisani wasu daga cikin mutanen suka tsere, yanzu haka mutum 16 ke hannunsu.

Sai dai jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ta ci tura sakamakon rashin amsa wayarsa.