✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace tsohon Kanar din soja a Zamfara

Maharan sun sace shi tare da ’ya’yansa biyu a lokacin da yake kan hanyar kai ziyara garinsu.

’Yan bindiga sun sace Kanar Lawal Rabiu Yandoto (mai ritaya) a kan hanyarsa ta zuwa garinsu, Yandoto da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Wata majiya ta bayyana cewa ’yan bindigar sun sace shi ne tare da ’ya’yansa biyu da kuma wasu.

“Maharan sun yi wa Kanar kwanton bauna da misalin karfe 6 na yamamcin ranar Lahadi, suka sace shi tare da ’ya’yansa biyu da kuma wasu mutum biyu,”  in ji majiyar.

Majiyar ta ce an ji karar harbe-harbe daura da shiga garin na Yandoto lamarin da ya tilasta mutane guje-guje domin tsira.

Ta bayyana cewa an gano maharan sun yi awon gaba da tsohon Kanar din ne bayan da mutane suka samu motarsa babu kowa a ciki.

Kakakin ’yan sandan jihar bai daga waya ba ballatana a ji ta bakinsa kan lamarin.