✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sake tare hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, sun kashe matafiya

Wurin dai ya yi kaurin suna wajen satar mutane.

A karo na biyu cikin sa’a 24, ’yan bindiga sun sake tare babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a Jihar Kaduna sannan suka karkashe matafiya.

Akalla matafiya shida ne aka sace yayin harin sannan aka yi awon gaba da wasu da dama.

Lamarin dai ya faru ne Unguwar Geda, da ke kusa da Zankoro, wajen misalin karfe 3:00 na yammacin Alhamis.

Wajen dai ya yi kaurin suna wajen satar mutane.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce har da kaninsa a cikin wadanda aka sace.

“Maganar da muke da kai yanzu, ina tabbatar maka da cewa mutum shida sun mutu, kuma ba mu san nawa aka sace ba. Kanina na cikin wadanda aka sace din.

“A zahirin gaskiya ma da yamman nan har masu garkuwar sun tuntubemu,” inji shi.

Kazalika, shi ma wani mazaunin yankin Udawa, Mohammed Umaru, ya ce an kashe kaninsa yayin harin.

‎“Muna cikin tashin hankali matuka, sun kashe kanina. Ba mu dade da dauko gawarsa ba don yi masa jana’iza,” inji shi.

Aminiya ta kuma gano cewa ’yan bindigar sun kuma fasa wata tawagar motocin da jami’an tsaro da ’yan sa-kai suka yi wa rakiya yayin harin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu wani jawabi a hukumance daga Gwamnatin Jihar ko daga Rundunar ’Yan Sanda, saboda Kakakin Rundunar, ASP Mohammed Jalige bai amsa kiran wayar wakilinmu ba.

‎A baya dai ’yan sandan sun ce sun sami nasarar kubutar da matafiya 40 da aka sace a kan hanyar ranar Laraba.