’Yan bindiga sun yaudari jama’a da kiran sallah sun kashe su | Aminiya

’Yan bindiga sun yaudari jama’a da kiran sallah sun kashe su

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga
    Abubakar Auwal, Sakkwato da Sagir Kano Saleh

’Yan bindiga sun kashe mutum shida tare da sace wasu da dama bayan sun yi wa mutanen garin Tureta ta Jihar Sakkwato tarko da kiran Sallar Subahi.

Luguden wutar da sojoji ke wa miyagun a Jihar Zamfara da ke iyaka da yankin Tureta ne ya tilasta musu tserewa, amma suka rika bin kauyuka suna kashe mutane suna garkuwa da wasu, suna harbin wasu.

Majiyarmu a Tureta ta ce da misalin karfe biyun dare, kafin wayewar garin Alhamis, ’yan bindiga suka far wa yankin, suka yaudari mutane da kiran Sallar Subahi.

“Bayan mutane sun fara fitowa, sun dauka lokacin sallah ne ya yi, sai kawai maharan suka rika bude musu wuta, suka kashe mutum shida, suka kuma yi awon gaba da wasu.

“Mun kadu kwarai da gaske, wasunmu ma sun fara kaura zuwa wasu wurare,” inji majiyarmu.

Aminiya ta gano cewa akwai mutane da dama kuma da ’yan bindigar suka harba da ke karbar magani a asibitin Tureta.

Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Maniru Dan’iya, ya ziyarci yankin domin yi musu ta’aziyya a ranar Alhamis, inda ya jaddada aniyar gwamanin jihar ta ganin bayan ayyukan ’yan bindiga a Jihar Sakkwato.

Ya kuma ce gwamnatin za ta dauki nauyin kulawa da wadanda aka kai asibitin.