✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi da dama a harin ba-zata

Fadar Shugaban Kasar ce ta tabbatar da harin

A ranar Talata ne ’yan ta’addan Boko Haram suka kashe sojojin Chadi da dama a wani harin kwanton bauna da suka kai a wani tsibiri da ke Tafkin Chadi, a cewar Zagazola Makama, wani kwararre kan harkokin tsaro a tafkin Chadi. 

Shugaban rikon kwarya na kasar ta Chadi, Mahamat Déby, ya ce sojojin da aka aike a matsayin masu kula da sansanin sojojin kasar na Chadi a tsibirin Bouka-Toullorom da ke tsakanin Ngouboua da Kaiga a tafkin Chadi sun fuskanci mummunan hari daga mayakan na Boko Haram.

Fadar Shugaban Kasar Chadi, ta sanar da duniya cewa, “A yau, harin ba-zata ya tabbatar da kasancewar ’yan Boko Haram a cikin tafkin Chadi babu kokwanto. ”

Shugaba Deby ya ce ya ga babbar barazana na tunkarowa, dalilin da ya sa ya tura adadi mai yawan gaske na dakarunsa na Baga-sola don zaburar da sojojin da kuma sake tsara shirin tunkarar wadannan ’yan ta’adda na Boko Haram.

A yayin da ake fuskantar wannan yanayi, shugaban ya jajanta wa iyalan sojojin da suka rasa ransu a fagen yaki tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Ya kuma umurci sojojin kasar da su dauki matakan da suka dace wajen kare iyakokin kasar.

Yayin da yake nanata kudurin kasar Chadi na kawar da ayyukan ta’addanci a kasar Chadi da kuma yankin, Shugaban Kasar ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki kwakkwaran mataki na wannan barazana ta hakika da kuma daukar matakin da ya dace.