’Yan Boko ne matsalar Najeriya —Sarkin Musulmi | Aminiya

’Yan Boko ne matsalar Najeriya —Sarkin Musulmi

Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmin Najeriya.
Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmin Najeriya.
    Rabilu Abubakar, Gombe

Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa ’yan boko da masu fada aji a kasar nan su ne matsalar Najeriya.

Alhaji Sa’ad Abubakar ya fadi hakan ne a yayin wani taron wanzar da zaman lafiya da gina kasa da Kwamitin Shirya Da’awah na Kasa ya shirya karo na uku a Jihar Gombe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, a yayin taron ne kwamitin wanda ya hada mabiya addinin Kirista da Musulmi ya tattauna matsalolin da ke hana ruwa gudu wajen samun zaman lafiya a kasar nan.

A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya kalubalanci shugabannin da cewa su koma wa littatafan su masu tsarki don samun ginshikin shugabanci na gari.

A cewarsa, muddin aka rasa kyakkyawan shugabanci to za a rasa zaman lafiya da hakan zai tarwatsa duk wani hadin kai a tsakanin al’umma.

Aminiya ta ruwaito cewa, kafin taron ne Sarkin Musulmin ya jagoranci bude wata hanya a garin Gombe da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya gina kuma aka sanya mata sunansa a Unguwar Gandu.