✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan daban daji sun kashe mutum bakwai a wani sabon hari a Neja

Aukuwar hare-haren ’yan daban daji ta zama ruwan dare a wasu sassa na Jihar Neja.

Mutum bakwai aka ruwaito ’yan daban daji sun kashe yayin da suka kai kari kauyen Yangalu na Karamar Hukumar Magama da ke Jihar Neja.

Maharan wadanda ba a san adadinsu mamaye kauyen ne haye a kan Babura inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi domin razanar da mutane.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, ’yan bindigar sun lalata dukiya da kayan abinci masu tarin yawa gabanin su arce daga kauyen.

Shugaban Karamar Hukumar Magama, Sufiyanu Yahaya, wanda ya kai ziyara kauyen da abin ya shafa, ya jajanta wa al’umma kan lamarin inda ya sha alwashin za a yi duk wata mai yiwuwa wajen inganta tsaro a yankin.

Aukuwar hare-haren ’yan daban daji ta zama ruwan dare a wasu sassa na Jihar Neja, inda a yanzu sun yi sanadiyar salwantar rayuka da dama da kuma raba mutane da muhallansu.

A halin yanzu ana fama da matsalar bayar da agajin da jin kai a jihar yayin da hare-haren ’yan bindigar suka fantsamar da mutane akalla kauyuka 70 na Jihar Neja.