✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi 4 sun shiga hannu a Delta

Sun yi kokarin tserewa bayan dubunsu ta cika amma jami'an tsaro suka cafke su.

’Yan sanda sun cafke wasu ’yan fashi hudu tare da kwace muggan makamai a wajensu.

Dubun ’yan fashin ta cika ne a wani shingen bincike, inda suka fada hannun jami’an ’yan sanda da ke yin sintiri.

  1. Gwamnati ta umarci kafafen yada labaran Najeriya su rufe shafukansu na Twitter
  2. An gano gawar mutum 97 da jirgi ya kife da su a Kebbi

“A ranar 5 ga Yuni, 2021, yayin da ’yan sanda ke bincike a kan titin Patani-Bayelsa, suka kama wata mota… da mutum hudu a cikinta wadanda ake zargin ’yan fashi ne.

“Suna hango jami’an ’yan sanda suka yi kokarin tserewa, amma nan take aka cafke su, an kuma samu bindiga kirar gida guda daya a tare da su’” inji kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta, DSP Edafe Bright.

Da yake bayani a Warri, DSP Edafe ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ari Ali, ya umarci duk jami’an ’yan sandan jihar da su zage damtse wajen yaki da muggan laifuka.

“Ya bukaci jama’a da su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanai da za su taimaka wajen rage yaduwar manyan laifuka a jihar,” inji Bright.