‘Yan fashi sun kashe wata budurwa a Abuja | Aminiya

‘Yan fashi sun kashe wata budurwa a Abuja

Budurwar da aka kashe, Marigayiya Mercy
Budurwar da aka kashe, Marigayiya Mercy
    Mardia Umar Da Bashir Isah

Wasu ‘yan fashi da makami sun kashe wata budurwa mai suna Mercy Jeremiah a lokacin da take kan hanyar zuwa wajen aiki a safiyar Talatar nan

Bayanai sun nuna an hallaka budurwar mai shekara 23 a kusa da kauyen Tudun Wada da ke yankin Lugbe a Abuja.

Binciken wakilanmu ya gano cewa, ‘yan fashin sun harbi Mercy da bindiga ne a ciki bayan da ta yi ihun barayi sun tare ta da misalin karfe 06:30 na safe a kan hanyarta ta zuwa wurin neman na abinci

Wannan danyen aiki ya jefa ‘yan uwan marigayiyar da ma sauran mazauna yankin cikin halin jimami, musamman wadanda suka yi ido biyu da ita kafin cim ma ajalinta.

Kafin rasuwarta, Mercy na zama ne tare da yayanta a yankin kauyen Zhidu kusa da Tudun Wada a Lugbe.

Tuni dai ‘yan uwan marigayiyar suka nemi a bi musu hakkin mutuwar ‘yarsu, inda suka soma shirye-shiryen mayar da gawarta zuwa jiharsu ta asali wato Kogi don binne ta.

Wani mai suna Mista Eze collins, mai sana’ar acaba a yankin da lamarin ya faru, na daya daga cikin wadanda suka yi kokarin kai wa Mercy dauki bayan da ya ji kuwarta.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, Jami’ar Hulda da Jama’a ta ‘Yan Sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce tuni bincike ya kankama.

Rashin kyawun hanyar wannan kauyen kan sa mazauna yankin takawa zuwa mararrabar Zhidu da Tudun kafin samun abin hawa, wanda a dalilin haka ne Mercy ta gamu da ajalinta.