✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Majalisa Sun Ba wa Hammata Iska A Senegal

’Yan majlisa a kasar Senegal sun dambace kan zargin wani babban malamin Musulunci da ke goyon bayan jam’iyyar adawa.

’Yan majlisa a kasar Senegal sun ba wa hamata iska kan zargin wani babban malamin Musulunci da ke goyon bayan jam’iyyar adawa.

Lamarin ya faru ne yayin kuri’ar jin ra’ayi kan kasafin ma’aikatar shari’a na badi, inda wata ’yar majalisa mai suna Amy Ndiaye ta zargi wani malamin addinin Mususlinci mai suna Serigne Moustapha da ke goyon ’yan adawa da yin karya da kuma rashin mutunta shugaban kasar, Macky Sall.

Wadannan kalamai nata ne suka tunzura wani dan majalisa daga bangaren adawar, har ya gaura mata mari, kamar yadda wasu hotuna da kamfanin dillancin labarai na AFP ya nuna.

Bayan ya mare ta ne kuma ta wurga masa kujera sannan ta fadi kasa, kafin masu mara mata baya su taimaka mata.

Daga nan ne kuma fada ya kacame tsakanin bangarorin biyu, har sai da shugaban majalisar ya dakatar da zaman.

Tuni wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da kungiyoyin kare hakkin mata suka yi tir da marin da aka tsinka wa ’yar majalisar, yayin da wasu daga cikin ’yan majalisar daga banagren adawa suka bayyana wa gidan Talabijin din kasar cewa dukkaninsu ba za su dawo aiki ba, har sai Ndiaye ta nemi afuwar malamin.