✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan sanda a Katsina sun ceto budurwa daga hannun ‘yan bindiga

Rundunar 'yan sandan Jihar ce ta tabbatar da hakan

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta dakile wani hari da masu satar mutane suka kai wata unguwa a Jihar, sannan suka ceto wata budurwa mai shekara 18 daga hannun maharan.

‘Yan bindigar dai sun kai hari ne a unguwar  Sakkwato Rima da ke birnin Katsina.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Jihar.

A ranar Laraba Ce dai da misalin karfe 2:30 na dare, ‘yan ta’addan dauke da bindigun AK47 suka far wa gidan wani mutum mai suna Abdullahi Esha da ke unguwar ta Rima a Katsina, in da suka sace wata budurwa mai shekaru 18.

“Jami’an Sintiri da kuma yaki da satar Mutane ta rundunar sun nufi inda lamarin ya faru ba tare da wani bata loakaci ba, sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar, amma a karshe sun samu nasarar kwato yarinyar,” inji Kakakin.

Ya kuma ce ‘yan bindigar sun bar mummunan aikin da ya kawo su domin tsira da rayukansu.