✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘’Yan sanda sun sako ’yan bindigar da aka kama a Zariya’

Mutanen yankunan Zariya sun bayyana dalilin karuwar hare-haren ’yan bindiga.

Mutanen yankin Zariya sun dora alhakin ta’azzarar hare-haren ’yan bindiga a kan sako wadansu masu garkuwa da mutane su biyar da suke zargin ’yan sanda sun yi a ranar 31 ga Mayun da ya gabata, bayan ’yan banga sun kama su sun mika wa ’yan sandan a watannin baya.

Mazauna yankin sun ce ana sako ’yan bindigar sai harkokin tsaro suka tabarbare a yankin, bayan sun samu saukin haka a lokacin da aka kama mutanen.

Mutanen yankin da Aminiya ta tattauna da su da suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce a mako biyu da suka gabata ’yan bindigar sun rika tsare hanyar Kaduna zuwa Zariya a-kai-a-kai suna fashi da sace mutane har lamarin yake kokarin cim ma birnin Zariya da kewaye.

Sun ce an fara kai harin ne a ranar 3 ga Yuni a Dumbin Rauga, dab da Kamfanin Taki na MATRID a hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Sai kuma washe-gari Juma’a 4 ga Yuni ’yan bindigar sun tare hanyar suka bude wa wata motar fasinja wuta suka kashe mutum biyu suka raunata biyar.

A ranar Alhamis din makon jiya kuma, da misalin karfe 1:00 na dare, ’yan bindigar suka sake tsare hanyar Kaduna, daidai Dumbin Rauga, daga baya suka ratsa ta cikin Dumbin Rauga da ke Gundumar Dutsen Abba suka shiga gida-gida, har da na Hakimin garin, Alhaji Falalu Usman, Maharin Zazzau.

Maharan sun kuma sun sace mata bakwai a unguwar, cikinsu har da wata mai tsohon ciki mai suna Adasiya da yara ’yan mata biyar da karamin yaro.

’Yan bindigar da aka sako

’Yan bindigar da aka sako a ranar Litinin 31 ga Mayu, a baya ’yan kungiyar sa-kai ne suka kama su bisa zargin su da kai hare-hare a Gundumar Dutsen Abba da kewaye.

Garuruwa da kauyukan da suke fuskantar sabuwar barazanar tsaro a yanzu su ne Unguwar Malam Atiku da Tankarau da Kamfanin Saye da Unguwar Kanawa da Majeru da Sabon Garin Kugu da Sabon Gida da Kasuwar Dutse da Unguwar Dallatu da Kafin Fulani da Mardanni da Rafin Yashi zuwa Kwaba.

Sai kuma yankin Dorayi da Buzai da ke Kofar Gayan da Dumbin Rauga, kafin lamarin ya danna zuwa dab da birnin Zariya.

Mutanen yankin sun ce tun da aka sako wadanda ake zargin, rashin tsaro ya sake dawowa fiye da baya a yankin Dutsen Abba da kewaye.

Kungiyar ’yan sintiri ta KADBS ce dai ta kama mutum shida da ake zargin da kai hare-hare da kashe mutane da garkuwa da mutane a yankin Dutsen Abba.

Aminiya ta ruwaito a ranar 4 ga Fabrairun 2021 cewa da misalin karfe 11:00 na dare wadanda ake zargin tare da wadansu da ba a kama su ba dauke da bindigogi kirar AK 47 suka auka wa kauyen Unguwar Hazo da ke Gundumar Dutsen Abba, inda suka kashe wani mai suna Musa Isa dan shekara 28 da Yusuf Sulaiman mai shekara 30.

Maharan sun harbi matan aure biyu masu suna Fatima Sulaiman (Magajiya) mai shekara 64 da Hafsatu Isa (Uwa) mai shekara 50.

Sun kuma kwace babura kirar ‘Boxer’ guda hudu, kuma sun kai hari gidan Kansilan Dutsen Abba, Alhaji Abdul’aziz Sani, a Unguwar Makada inda suka sace matarsa Samira Abdul’aziz da wata matar aure mai suna Halima M. Sani.

Bayan harin ne ’yan Kungiyar Sintiri ta Jihar Kaduna da ke Unguwar Mai Turmi a Karamar Hukumar Igabi suka tsare masu garkuwar inda suka ceto wadanda aka sato da kuma kwato baburan hudu.

Kungiyar ta kama Mu’azu Sani wanda kanen Kansilan ne da Mubarak Adamu da ke Unguwar Makada da Faisal Shehu, wani Bafulatani mazaunin Unguwar Malam Atiku da Yunusa Audi da Sani Igwa da kuma Abubakar Muhammad, wadanda aka mika su ga Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna don ci gaba da bincike da tabbatar da an hukunta su, amma sai ’yan sandan suka sako su.

Kansilan Dutsen Abba Alhaji Abdul’aziz Sani, ya tabbatar wa Aminiya cewa an sako wadanda ake zargin, ya ce daga cikin mutum shida da aka kama, kanensa ne kawai ba a sako ba.

Ya ce, ganin wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu da kansu a gaban al’ummar yankin, kuma an samu wadansunsu da makamai, sakinsu ya ba jama’a mamaki.

Abdul’aziz ya ce bayan da aka kama su, yankin ya samu saukin irin wannan ta’addanci.

Sai ya nuna damuwa a kan sake tabarbarewar tsaro bayan sako su, inda ya ce al’amuran tsaro sun sake sukurkucewa a yankin.

A don haka al’ummarsu suna cikin damuwa, a daidai wannan lokaci da suke shirin fara aikin gona.

Kasilan ya ce rashin tsaro na iya hana manoman yankin da baki masu zuwa gudanar da aikin gona a bana.

Za ku ji dalilin sakin masu garkuwar —’Yan sanda

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige, kan sako wadanda ake zargin, sai ya nemi ta ba shi sunayen wadanda aka sako din.

Bayan aike masa da sunayen, ya kira inda ya tabbatar da cewa ya karbi sunayen kuma ya yi alkawarin zai kira don ya yi bayanin dalilan da suka sa aka sako su.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai ba da bayani a kan dalilan sako wadanda ake zargin ba.

Mazauna kauyukan da ke kusa da birnin Zariya, fadar Masarautar Zazzau da na cikin garin, suna fama da matsalar ’yan bindiga da suke kai musu hare-hare suna sace su suna yin garkuwa da su.

’Yan bindiga na farautar mu —Sarkin Zazzau

Munin hare-haren ne ya sa Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, ya kira taro da shugabannin tsaro na Jihar Kaduna, inda ya shaida musu cewa a kusan kullum sai ’yan bindigar sun kai hari a birnin da kewayensa.

A ranar Alhamis din makon jiya ne da misalin karfe 10:00 na dare,  ’yan bindigar sun kutsa cikin Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Nuhu Bamalli mallakar Gwamnatin Jihar Kaduna da ke yankin Dumbin Rauga  a hanyar Zariya zuwa Kaduna, suka kashe dalibi daya suka raunata daya, sannan suka sace malamai biyu da dalibai takwas.

Dalibin da ya rasu mai suna Ahmad Abdulhameed, yana karantun babbar diploma ne a fannin kididiga.

Wanda aka harbe shi a cinya mai suna Haruna Isiyaku Duna, yana karatu ne a fannin kididdiga a kwalejin.

Daga cikin malaman da ’yan bindigar suka sace, akwai Mista Habila Nisa’i, malami a fannin koyar da fannonin ilimi, sai Malam Adamu Shehu Shika da yake fannin tattalin arziki da kudi.

Sai dai ’yan bindigar sun sako matar Malam Ahmad Abdul da ’ya’yansa kanana biyu saboda ta kasa tafiya sakamakon tsoho ciki.