✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a Ribas

’Yan bindiga sun kashe sojoji hudu a bakin aiki a Jihar Ribas

’Yan bindiga sun kashe sojoji hudu da suke rakiyar wasu ma’aikatan kamfanin mai a Jihar Ribas.

Mukkaddashin Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta 6, Manjo Danjuma Jonah, ya ce an yi wa sojojin kwanton bauna ne a yankin Enweh West da ke Karamar Hukumar Ahoada ta Gabas ta Jihar.

Ya ce  a yayin musayar wuta a ranar Talata ne sojoji hudu suka kwanta dama, biyu daga cikin ma’aikatan kamfanin man kuma ba a gan su ba.

Manjo Jonah ya ce an yi wa sojojin  kwanton bauna ne a kan hanyar Amungboro zuwa Emuphan, inda “maharan suka tsere ta Kogin Orashi.

“Sojoji na ci gaba da yin sharar wurin domin kamo maharan da kuma gano ma’aikatan kamfanin man da ba a gani ba.

“Baban Kwamnadan Runduna ta 6 Manjo-Janar Jamal Abdussalam, ya jinjina wa sojojin da suka rasu, tare da yin Allah-wadai da harin,” in ji Danjuma Jonah a sanarwar da ya fitar a daren Talata.

Daga nan sai ya roki al’ummar yaankin su taimaka wa sojoji da bayanai da za su  taimaka a kamo maharan.