✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan tawayen Houthi sun kashe sojojin Sudan 14 a Yemen

Sojojin sun rasu ne a harin da mayakan Houthi suka kai wani sansanin sojojin hadin gwiwar kasashe Larabawa

’Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun kashe sojojin Sudan 14 a harin da mayakan suka kai a iyakar kasar na yankin Arewa maso Yammaci da kasar Saudiyya.

Sojojin sun gamu da ajalinsu ne bayan mayakan na Houthi sun kai hari kan sansanin sojojin hadin gwiwar kasashe Larabawa na Haradh da ke lardin Hajja na kasar.

Sojojin Sudan din da aka kashe na daga cikin rundunar hadin gwiwar kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta a yaki da ’yan tawayen Yemen, wadanda kasar Iran ke mara wa baya.

Tun shekarar 2015 gamayyar kasashen Larabawan ke yaki da ’yan tawayen Houthi domin kare halastacciyar gwamnatin Yemen da mayakan suke neman hambararwa.

Sudan — wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a cikin kasashen da suka fi fama da yunwa — ta tura dubban sojojinta da mayakanta na sa-kai (Janjaweed) zuwa yakin na Yemen.

A shekarar 2019, gwamantin rikon kwaryar Sudan ta ce kasar ta rage yawan sojojinta da ke Yemen daga mutum 15,000 zuwa 5,000.

A kwanakin baya, wasu ’yan Sudan sun yi zanga-zanga a birnin Khartoum, inda suka zargin wani kamfanin tsaro daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da daukar ’yan uwansu aikin gadi, amma ya tura su fagen yaki a kasashen Libya da Yemen.

Tun a shekara 2014 ake yakin Yemen, inda mayakan Houthi suka kwace Sanaa, babban birnin kasar, wanda kuma ya jefa kasar cikin tashin hankali da wahalhalu.

Muliyoyin ’yan kasar sun yi kaura daga gidajensu a sakamakon haka, a yayin da a halin yanzu mutum takwas a cikin kowane mutum 10 a kasar ke bukatar taimakon bukatun rayuwa.

A watan Nuwamba, Hukumar Kula da Ci Gaban Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta ce an kashe kimanin mutum 377,000 a rikicin na Yemen.

Ta ce, kusan kashi 60 cikin 100 na mamatan sun rasu ne a sakamakon yunwa, cututtuka da rashin tsaftaccen ruwan sha, a yayin da yakin ya kashe mutum 150,000 kai tsaye.