✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan tawayen Houthi sun yi wa Saudiya tayin sulhu

Mayakan Houthi sun yi alkawarin bude filin tashi da saukar jiragen sama na Sana’a, babban birnin Yemen.

’Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun gabatar da tayin tsagaita wuta da tattaunawar zaman lafiya domin kawo karshen yakin da suka shafe shekaru kusan 7 suna gwabzawa da sojojin kawancen da Saudiya ke jagoranta.

Hakan dai na kunshe cikin wata sanarwa da wani babban jami’in Saudiyya ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Asabar.

Cikin tayin da suka gabatar, mayakan na Houthi sun yi alkawarin bude filin tashi da saukar jiragen sama na babban birnin Yemen, wato Sana’a, da kuma babbar tashar jiragen ruwa ta Hodeida.

Bukatar ‘yan Houthin na zuwa ne kwana guda bayan hare-haren da suka kaiwa sassan Saudiya da makamai masu linzami, ciki har da wata cibiyar mai a birnin Jeddah, lamarin da ya haifar da mummunar gobara da ta haifar da fargaba a tsakanin masu halartar gasar tseren motoci na Formula One.

Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa a makon jiya ne dai ’yan tawayen da Iran ke marawa baya suka yi watsi da tayin tattaunawar sulhu a Riyadh, babban birnin Saudiya.