✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU ta shiga ganawar sirri da Gwamnatin Tarayya

Wakilan ASUU da na Gwamnatin Tarayya sun koma teburin sulhu.

A halin yanzu wakilan Gwamnatin Tarayya da na Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya, ASUU, sun shiga ganawar sirri domin ci gaba sasanci da nufin kawo karshen yajin aikin kungiyar da ya ki ci ya ki cinyewa.

An fara gudanar da taron ne da misalin karfe 5.13 na Yammacin Alhamis, wanda Ministan Kwadago da Ayyuka, Dokta Chris Ngige ke jagoranta.

Aminiya ta ruwaito cewa wannan zama na zuwa ne bayan dage zaman sulhu da bangarorin biyu suka yi har karo biyu a makonnin da suka gabata.

A watan jiya ne Gwamnatin Tarayya ta mika wuya inda ta amince da tsame malaman jami’ar daga cikin ma’aikatan da za ta rika biya a karkashin sabon tsarin albashin bai-daya na IPPIS.

A zaman sulhun da ta yi da kungiyar malaman jami’o’in a watan Nuwamban da ya gabata, gwamnati ta amince za ta sauke nauyin bashin da ke kanta na biyansu albashin watan Fabrairu zuwa Yuni a bisa tsohon tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnati na GIFMIS.

Sai dai gwamnatin ta ce tsame mambobin ASUU daga tsarin biyan albashin na IPPIS na wucin gadi, inda a halin yanzu ake ci gaba da kirdadon tantace nagartar sabon tsarin biyan albashin na UTAS da kungiyar malaman ta gabatar.

Ana iya tuna cewa gwamnatin tarayyar a yayin zaman sulhu da ya gudana tsakaninta da kungiyar a ranar 27 ga watan Nuwamba, ta yi alkawarin biyan kungiyar Naira biliyan 40 a matsayin alawus din malamai da kuma naira biliyan 30 domin farfado da jami’o’in kasar.