✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a biya inshorar N13bn ga ’yan sandan da suka mutu

’Yan Sanda 318,319 da suka rasu ne za su ci gajiyar shirin tsakanin shekarar 2022 da 2023

Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da biyan Naira biliyan 13.3 a matsayin inshora ga ’Yan Sandan Najeriya da suka mutu.

Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi, ya ce jami’ai 318,319 ne za su ci gajiyar shirin tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023.

A cewarsa, an samar da shirin inshorar ne don karfafa wa ’yan sanda gwiwa a aikin da suke yi babu dare, babu rana don kare rayuka da dukiyar ’yan kasa.

Ya bayyana haka ne ga manema labarai bayan kammala taron Majalisar a Fadar Shugaban Kasa ranar Laraba.

Taron Majlisar ya gudana ne karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.