✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a dauki ma’aikata 2,000 don yakar shaye-shaye a Zamfara

Gwamnatin Zamfara ta amince da daukar ma’aikata 2,000 da za su yaki ayyukan daba da shaye-shaye a jihar. Shugaban kwamitin yaki da daba na jihar,…

Gwamnatin Zamfara ta amince da daukar ma’aikata 2,000 da za su yaki ayyukan daba da shaye-shaye a jihar.

Shugaban kwamitin yaki da daba na jihar, Bello Bakyasuwa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau a ranar Alhamis.

“Gwamna Matawalle ya ba mu umarnin daukar ma’aikata 2,000 maza da mata, don inganta bangaren tsaron al’umma ba tare da nuna bangaranci ko ra’ayin siyasa ba.

“Yanzu haka mutane 6,000 ne ke neman aikin, amma dole 2,000 za mu tantance mu diba.

“Wannan duk na daga cikin kudirin gwamnatin na fadada ayyukanta na yaki da daba da shaye-shaye a tsakanin matasa, a dukkanin kananan hukumomin 14 da ke Zamfara”, in ji Bakyasuwa.

Gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya kafa kwamitin ne da zummar yakar daba da shaye-shaye, da sauran laifuka da suka addabi jihar.