✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Za a jima ba a maye gurbin abin da aka sace a Abuja ba’

Barnar da bata-garin da suka fake da zanga-zangar #EndSARS suka yi ta wuce misali

Shugaban Hukumar Agajin ta Yankin Birnin Tarayya, Alhaji Abbas Idris, ya bayyana barnar da masu fasa dakunan ajiye kayan abinci suka yi a Abuja a matsayin abun da za a jima ba a maye gurbinsa ba.

Abbas ya ce bata-garin sun fake da zanga-zangar #EndSARS sun lalata daukacin abun da aka adana don raba wa mabukata, kuma sun sace har da kayan koyar da sana’o’i da aka tanadar.

A hirar da Aminiya ta yi da shi kai-tsaye a shafinta na Facebook a Larabar nan, shugaban hukumar na FEMA ya ce, “A nan Abuja mun bi tsari mai kyau wurin rabon kayan inda muka je gida-gida muka raba a lokacin kullen coronavirus.

“Abun da aka gani da sunan kayan tallafi kungiyoyi ne suka kawo mana, muna dab da rabawa washegari aka far wa kayan aka kwashe”.

A amsarsa ga tsokacin masu kallon shafin Aminiya a lokacin tattaunawar, Abbas ya ce hukumarsa na maraba da duk mai son ganin kwakwaf kan tsarin da ta bi wurin rabon kayan, su nuna masa komai daki-daki.

Don ganin yadda ta kaya, za ku iya kallon cikakkiyar hirar a shafinmu na Facebook mai suna aminiyatrust.