✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a biya wa nakassau 2,600 kudin jarrabawa N32m a Kano

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta amince a fitar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 32 domin biyan kudin jarrabawa ga dalibai 2,595

Majalisar Zartarwa ta Kano ta amince a fitar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 32 domin biyan kudin jarrabawa ga dalibai 2,595 masu bukata ta musamman ’yan asalin jihar.

Jarrabawoyin da za a biya wa daliban sun hada da ta NECO, NBAIS da kuma ta WAEC.

Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya sanar da haka jim kadan da kammala taron majalisar a Fadar Gwamnatin Kano ranar Alhamis.

A cewarsa, “Majalisar ta amince a kashe Naira 11,000 ga dalibai 2,595 masu bukata ta musamman da aka tantance domin rubuta jarrabawar NECO, adadin kudin ya kai Naira miliyan 28.5; sai kuma Naira miliyan daya da dubu dari takwas da za a kashe wa masu jarrabawar NBAIS.”

Garba ya kuma ce majalisar amince a kara yawan kudaden da aka ware domin samar da kayan aiki a asibitin garin Kafin Maiyaki na Karamar Hukumar Kiru a kan Naira miliyan 132.7 domin inganta harkar lafiya.

Kazalika, kwamishinan an amince a kashe Naira miliyan 21 domin sayo litattafai 11,800 kan ‘Fasahar Bayen Dabbbobi da Kiwon Kifi’ don a farfado da karatun aikin gona a jihar.