✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a yi wa almajiran da aka kama a Kaduna gwajin COVID-19

Gwamnatin Kaduna ta yi awon gaba da almajiran gidan Sheikh Dahiru Bauchi

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta yi wa almajirai 160 da ta kama a daren Juma’a gwajin cutar COVID-19 sannan ta isa keyarsu zuwa jihohinsu.

A cikin dare ne dai jami’an kwamitin kar-ta-kwana kan yaki da COVID-19 na Jihar Kaduna suka isa a gidan babban malamin Darikar Tijjaniya, Shaikh Dahiru Usman Bauchi a unguwar Asikolaye suka tafi da yaran.

Tawagar da ta ta kunshi sojoji, ’yan sanda, da Hukumar Kula da Hanyoyi da Muhalli ta Jihar (KASTELEA) sun loda yaran ne a motoci zuwa sansanin alhazai.

Kakakin Gwamnatin Kaduna, Muyiwa Adekeye ya ce za a dauki bayanan yaran, a yi musu gwajin lafiya ciki har da na COVID-19 kafin a mayar da su jihohinsu iyayensu su ci gaba da kula da iliminsu.

Wani malami a makarantar allon, Allaramma Nasiru Ibrahim ya yi tir da samamen da aka kai gidan Shaikh Dahiru Bauchi wanda ya ce babban kuskure ne.

Amma Muyiwa ya bayyana a ranar Juma’a cewa wasu daga cikin yaran kanana ne sosai da ba za ma su iya bayar da bayan kansu ba.

Ya ye wuraren da aka kama yaran sun saba umarnin gwamnain jihar na rufe makarantu a watan Disamba, 2020, kuma ba su da izinin ajiye almajirai a makarantu ko gidajen yara.

A cewarsa, Gwamnatin Jihar Kaduna ta gano wuraren da ake ajiye almajirai ta kuma mayar da yara 31,092 jihohinsu tun daga ranar 30 ga watan Maris, 2020 da Kungiyar Gwamnanon Arewa ta amince ta kawo karshen mummunan halin da ake jefa yara a ciki da sunan almajiranci.

Ya ce yaran su 160 sun fito ne daga jihohi 13 na Arewaci da Kudancin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nihar, Burkina Faso da Jamhuriyar Benin.

Kakakin Gwamnatin Jihar ya kuma yi kira ga iyaye da su dauki nauyin da Allah Ya dora musu tarbiyyantar da ’ya’yansu da kuma kula da walwalarsu ba su yi watsi da su ba.

Jihohin da yaran suka fito sun ne Kebbi: 16,  Abuja 2, Katsina 15,  Kano 15,  Zamfara 8,  Sokoto 1, Nasarawa 12,  Niger 5.

Sauran jihohin su ne Kwara 4,  Kogi 2,  Oyo 2,  Kaduna 68,  Jamhuriyar Nijar 5,  Burkina Faso 3, Jamhuriyar Benin 1.