✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za mu kafa gwamnatin Musulunci a Katsina —NNPP

NNPP ta yi alkawarin soke harajin da aka dora wa takawa a Jihar Katsina.

Jam’iyyar NNPP ta yi alkawarin kafa ingantacciyar gwamnati wadda za ta tafi a kan tsarin Musulunci idan ta ci zaben Gwamnan jihar Katsina da ke tafe.

Mataimakin dan takarar gwaman jihar na Jam’iyyar NNPP, Muttaqa Rabe Darma, ne ya sanar da haka tare da cewa gwamnatinsu za ta soke harajin da aka dora wa takawa a Jihar Katsina.

Ya yi alkawarin ne a Zauren Al’Umma da kafafen yada labarai na Media Trust da sauransu suka shirya domin ganawa da ’yan takarar gwamnan jihar a Katsina.

Ya yi jawabin ne da yake wakiltar dan takarar gwamna na jam’iyyarsa, Injiniya Nura Khalil.

Ya shaida wa taron cewa matsalolin Najeriya suna da alaka ta kai-tsaye da rashin ingantacciyar gwamnati me kyakkyawan tsari.

Ya ce a karkashin gwamnatinsu, za su bunkasa sha’anin kudin shiga ta yadda abin da jihar za ta samu daga Gwamnatin Tarayya ba zai wuce kashi 20 cikin 100 ba na kudin shiga.

Darma ya bayyana cewa za su cimma hakan ba tare da dora wa talaka haraji ba.