✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu murkushe cutar zazzabin cizon sauro zuwa 2025 — WHO

Sama da kashi 90 na mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da ita na fitowa ne daga Afirka.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta kaddamar da shirin kawar da cutar zazzabin cizon sauro daga doron kasa nan da shekarar 2025.

Sanarwar da Hukumar ta fitar a shafinta na yanar gizo ranar Laraba, ta ce za ta taimaka wajen dakile yaduwar cutar a wasu kashe 25 da ke fama da matsalar a yanzu.

Wannan rahoto na zuwa ne kafin ranar bikin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da za a yi ranar 25 ga watan Afrilu kamar yadda aka saba duk shekara.

Dokta Pedro Alonso, Daraktan shirye-shirye a kan yaki da zazzabin cizon sauro na Hukumar, ya ce sun yi nasarar taimaka wa kasashe 21 wajen magance cutar a karkashin shirin da aka kaddamar a shekarar 2017, kuma takwas daga cikin sun samu nasara da suka hada da China, Iran, Paraguay, El Savador, Malaysia, Algeria, Belize da Cape Verde.

WHO ta ce a yanzu akwai wasu kasashe 25 da ke da kwarin gwiwar kawar da cutar baki daya daga cikin nan da shekarar 2025 wanda ta ce za ta taimaka musu wajen samun nasarar.

Ta ce wadannan kasashe za su samu taimako na musamman da kuma kwarewar masana wajen sun cimma wannan nasara da suka sa a gaba.

Shugaban Hukumar, Dokta Tedros Adhanom, ya ce kasashen da a yanzu suka samu nasarar kawar da cutar da cikinsu, a baya cutar ta kasance musu alakakai da bayan sun tashi tsaye sun nuna wa duniya cewa ana iya murkusheta daga doron kasa.

Rahotan hukumar na watan Nuwambar bara ya ce akalla mutane miliyan 229 suka gamu da cutar da ke da nasaba da zazzabin cizon sauro a shekarar 2019, inda sama da kashi 90 na mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da ita na fitowa ne daga Afirka, kuma sama da 265,000 daga cikin su yara ne kanana.