✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zaben Ondo: ‘PDP za ta maimaita nasara kamar yadda ta yi a Oyo da Edo’

Dan takarar Gwamnan Jihar Ondo na jam’iyyar PDP, Eyitayo Jegede ya ce jam’iyyarsa ce za ta lashe zaben Gwamnan Jihar tamkar yadda ta lashe a…

Dan takarar Gwamnan Jihar Ondo na jam’iyyar PDP, Eyitayo Jegede ya ce jam’iyyarsa ce za ta lashe zaben Gwamnan Jihar tamkar yadda ta lashe a jihohin Oyo da Edo.

Dan takarar gwamnan a zaben da za gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba, ya bayyana haka ne a sa’ilin da ya ziyarci masarautar Sarkin Hausawa Ore a ranar Juma’a 25 ga watan Satumba inda ya sha alwashin gyara hanya zuwa masarautar wacce ta hade da babbar kasuwar goro ta garin Ore.

Eyitayo Jegede wanda ya lalacewar hanya ta sanya ya yi tattaki da kafa tare da tawagarsa har zuwa fadar Sarkin Hausawan, Ire Alhaji Abdullahi Bagobiri, ya sha alwashin share masu hawaye da zarar ya cimma nufinsa na zama gwamna a jihar.

Ya ce, “Al’ummar Hausawa mutane ne masu muhimmanci a daukacin jihar Ondo wanda a dalilin haka na kawo musu ziyara.”

“Baya ga hanyar da zan gyara masu zan kuma bai wa ‘yan kasuwa jari domin bukasa sana’arsu don habaka tattalin arzikin jiharmu tare da samar da guraben ayyukan yi da zarar Allah ya bamu nasara”, inji shi.

Da yake karbar bakuncin dan takarar Gwamnan, Sarkin Hausawan Ore Alhaji Abdullahi Bagobiri ya ba shi tabbacin goyon bayan al’ummar Arewa kasancewarsa mutumin kirki.

“Kai ne ka sanya tsohon Gwamna Olusegun Mimiko ya yi mana ayyukan alheri don haka za mu mara maka baya da kuri’unmu dari bisa dari,”inji Bagobiri.

Cikin tawagar dan takarar gwamnan ta har da tsohon Gwamnan Kano a lokacin mulki soji, Kanal Aminu Isa Kwantagora mai ritaya.