✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zakir Naik ya ba Falasdinawa tallafin N383m

Zakir Naik ya sadaukar da Naira miliyan 383 domin agaza wa Falasdinawa a Zirin Gaza, ya kuma jinjina wa kungiyar Hamasa kan fafutikar ’yacin Falasdinu

Fitaccen malamin Musulunci na duniya, Dokta Zakir Naik, ya ba da gudummawar Naira miliyan 381 domin tallafa wa Falasdinawa  a Zirin Gaza.

Zakir Naik a yayin ziyararsa Najeriya daga Indiya, ya la’anci kisan da Isra’ila ke wa Falasdinawa a Zirin Gaza, inda ya bayyana kungiyar a matsayin mai fafutikar ’yacin kasar Falasdinu..

Shahararren malamin ya bayyana kungiyar Hamas a matsayin mai gwagwarmayar kwato ’yancin Falasdinu.

Da yake lacca a yayin rufe makon Sheikh Usmanu bin Fodio da ya gudana a Sakkwato, Zakir Naik ya ce, “Hamas tana yaki ne da mamaya Falasdinu da Isra’ila ta yi.

“Isra’ila ta shafe sama da shekaru 70 tana yi wa Falasdinawa kisan gilla tana kuma raba da gidajensu da kasarsu.”

Ya bayyana cewa abin da Hamas ke yi ba shi da bambanci da wanda tsohon shugaban Amurka, George Washington da Nelson Mandela na Afirka ta Kudu suka yi, kuma babu wanda ya kira shugabanin ’yan ta’adda. Saboda haka Hamas masu neman ’yanci ne ba ’yan ta’adda ba.

“A wata guda Isra’ila ta kashe dubban Falasdinawa kuma akasarinsu wadanda ta kashe kananan yara da mata da kuma tsofaffi ne.

“Muna Allah-wadai da abin da Isra’ila ke yi kuma muna kiran kasashen duniya su fito su la’anci abin Isra’ila ke yi,” in ji shi.

Daga nan malamin ya sadaukar da Dala 320,000, kimanin miliyan N383, a matsayin gudummawarsa domin sama wa Falasdinawa kayan tallafi.

Malamin ya bayyana cewa kudin da ya sadaukar, diyya ce da kotu ta umarci karamin ministan kudin kasar Malysia ya biya shi, shekaru 20 da suka gabata.

“Na sadaukar da su ga Falasdinawa,“ in ji shi.