✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zamfara: Mahara sun bindige ma’aikatan kwaleji

Sun bude wa ma'aikatan Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya wuta a kofar gida

’Yan bindiga sun harbe ma’aikan Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Kaura Namoda, Jihar Zamfara.

’Yan bindigar sun kai farmakin ne a rahar Laraba inda suka bindige ma’aikata biyu na kwalejin a gidansu.

Aminiya ta gano cewa ’yan bindiga kusan shida ne suka kutsa rukunin gidaje masu saukin kudi da ke Kaura Namoda, suka fada gidan wani mai suna Nazifa suka bukaci ya bude musu.

Da ya ga haka, sai ya ki budewa, sannan yi ihun neman jama’a su kawo masa dauki.

“Daga nan sai ’yan bindigar suka gudu, sai ya kira wani makwabcinsa suka tsaya a kofar gida suna tattaunawa game harin.

“Ba su sani ba, ashe ’yan bindigar na boye ne a wani kango, ba a jima ba suka bude musu wuta su biyun,” inji wani mazaunin unguwar.

Shugaban Kwalejin, Yahaya Muhammad Bande ya bayyana takaicinsa game da harin, wanda ya kira dabbacin.

Tuni dai aka binne mamatan.