✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan dawo da martabar ilimi a Zamfara — Dauda Lawal

A makon da ya gabata ne gwamnan jihar ya ayyana dokar ta-baci kan bangaren ilimi a jihar.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dawo da martabar ilimi a jihar.

Da yake bayar da tabbacin a wajen kaddamar da gine-gine da gyaran makarantu a hukumance, Gwamna Lawal ya jaddada kudirinsa na farfado da ilimi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce gwamnatin jihar ta bai wa ilimi muhimmanci domin cika alkawuran yakin neman zaben da ta dauka.

A cewarsa, fara ayyukan ya yi daidai da dokar ta-baci da gwamnatin ta ayyana a fannin ilimi.

Ya ce: “Lokacin da ake gabatar da wasikun bayar da aikin gine-gine da gyara makarantu a Jihar Zamfara, Gwamna Lawal ya bayyana kudirinsa na inganta fannin ilimi gaba daya.

“Aikin kaddamar da gini da gyara azuzuwa ne da samar da kayan karatu ga dalibai da malamai a makarantunmu, duk a bisa tsarin dokar ta-baci da gwamnati ta ayyana.

“Shahararrun ‘yan kwangilar ‘yan asalin jihar nan ne za su gudanar da ayyukan.

“Ayyukan sun hada da sake gyara makarantun da suka lalace gaba daya a fadin kananan hukumomin 14.

“ Baya ga sabunta wasu da suka hada da makarantun Tsangaya da ke shiyya uku;, Anka, Kaura Namoda da Gusau.

“Domin aiwatar da wadannan ayyuka, jimillar N4,346,450,209.19 gwamnati ta ware. An zabi ‘yan kwangilar da za su yi aikin, bisa la’akari da kwarewarsu.

“Aikin ya kunshi ginawa da kuma gyara makarantu 245 a fadin kananan hukumomi 14 da ke jihar. Bugu da kari, za a samar da tebura masu kujeru biyu guda 9,542 ga daliban makarantu a fadin kananan hukumomin 14.”