✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zan yi sauye-sauye a bangaren tsaro —Buhari

Buhari ya ce zai yi sauyi a duk inda bai gamsu ba a gwamnatinsa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa manyan hafsoshni taro shirinsa na yin sauye-sauye a tsarin tsaron Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin manyan hafsoshni tsaron inda suka gabatar masa da rahoton ayyukansu a ranar Talata.

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ya ce Buhari ya shaida wa Manyan Hafsoshin Tsaron cewa zai ci gaba da yin canje-canje a wurin da bai gamsu ba a bangaren na tsaro.

Monguno, wanda ya yi wa manema labarai bayani bayan zaman a Fadar Shugaban Kasa, ya Buhari ya bayyana wa hafsoshin tsaon matsayinsa ne bayan sun gabatar masa da nasarorin da sojoji suka samu a yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Shugaban Kasar ya saurari bayanan nasu ne bayan alkawarin da ya yi a ranar 19 ga Agusta 2021, na yin duk mai yuwuwa don magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.

Idan ba a manta ba a lokacin wancan zama, Shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa na barin mulki a 2023, ba tare da ya gaza ba musamman a bangaren tsaro.

Monguno ya ce Buhari ya nuna farin cikinsa kan nasarorin da rundunonin tsaro suke samu a halin yanzu a yakin da suke yi da masu tayar da kayar baya, ’yan fashi, masu garkuwa da mutane, da sauran masu aikata miyagun laifuka a sassa daban-daban na kasar nan.

Mahalarta taron na ranar Talata sun hada da Ministan Tsaro, Janar Bashir Magashi (mai ritaya) da Ministan Shari’a, Abubakar Malami da manyan Hafsoshin Soji wadanda Babban Hafsan Soji, Janar Lucky Irabor ya jagoranta.