✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zanga-zangar kungiyar kwadago raini ne —Ministan Shari’a

Ministan Shari’a Lateef Fagbemi ya cewa zanga-zangar da kungiyar kwadago ta NLC da TUC suke shirin gudanarwa raini ne ga bangaren shari'a

Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ya bayyana cewa zanga-zangar da kungiyar kwadago ta NLC da TUC suke shirin gudanarwa raina umarnin kotu ne.

Ministan shari’an ya sanar da haka ne a wasikar da ya aike wa lauyan kungiyar kwadagon game da shirin zanga-zangar da za a gudanar ranar talata.

A cewarsa, zanga-zangar ta ta’allaka ne a kan tsadar man fetur da na katan masarufi, jin dadin ma’aikata, da kuma tallafin cire tallafin man fetur da wasu tsare-tsaren gwamnati kuma bangarorin sun kulla yarjejeniyar  a kai.

“Ku tuna cewa wadannan batutuwa su ne tushen shari’ar da ke gaban Kotun Masana’antu ta Ƙasa.

“Bayan gabatar da korafe-korafe ga kotu, masu shigar da kara ba su da hurumin yin zanga-zanga a kan batutuwan, saboda yin hakan babban wulakanci da cin fuska ga bangaren shari’a.

“Saboda haka zanga-zangar da ake shirin yi a duk fadin kasar ya saba wa umarnin wucin gadi da kotu ta bayar a 2023 a shari’ar tsakanin Gwamnatin Tarayya da NLC da TUC, inda aka hana su kowane irin zanga-zanga ko shiga yajin aiki,” in ji shi.

Shugaban NLC, Joe Ajaero da ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da gudanar da zanga-zangar da aka shirya domin a cewarsa, “zanga-zangarmu ta lumana ce domin adawa da tsadar rayuwa da al’ummarmu ke fama da ita.