✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum zai gina gidaje 500 domin ’yan gudun hijira a Bama

Za a kuma gyara gidaje 1,000 da hare-haren Boko Haram suka lalata

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ba da umarnin gina gidaje 500 a garin Nguro Soye, da ke Karamar Hukumar Bama domin tsugunar da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Zulum ya kuma sa gyara wasu gidaje 1,000 a garin da aka lalata a hare-haren kungiyar.

Ya ba da umarnin gudanar da ayyukan ne a lokacin da ya ziyarci Bama a ranar Talata.

A lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Shehun Bama, Shehu Umar Ibn Kyari Ibrahim El-kenemi, gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da ganin karin yara a jihar na samun halartar makarantu.

Ya kuma amince da bukatar da Shehun Bama ya gabatar mas na kara tallafa wa manoma gabanin faduwar damina da ke kara karatowa a Jihar.