✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A karo na 6, an sake tsawaita wa’adin hada layukan waya da lambar NIN

Yanzu haka mutum miliyan 59.8 ne suka hada layukansu da lambar.

Gwamnatin Tarayya ta sake kara wa’adin hada layukan waya da lambar Shaidar Zama dan Kasa (NIN) har zuwa ranar 31 ga watan Oktoban 2021.

Wannan dai shi ne karo na shida kenan da ake kara wa’adin tun lokacin da gwamnatin ta sanar da fara matakin a bara.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) da takwararta ta Shaidar Zama dan Kasa (NIMC) suka fitar ranar Lahadi, gwamnatin ta ce daukar matakin ya biyo bayan bukatar da masu ruwa da tsaki suka gabatar musu kan isa zuwa kauyuka masu wahalar shiga da ’yan kasahen waje da kuma ’yan Najeriya mazauna ketare.

Sanarwar, wacce masu magana da yawun hukumomin biyu, Ikechukwu Adinde da Kayode Adegoke suka fitar ta ce tsawaita wa’adin zai kuma taimaka wajen magance kalubalen yin rijistar a makarantu da asibitoci kamar yadda alkaluma suka nuna.

“Hakan ya biyo bayan nazarin ci gaban shirin da ake samu, wanda ya nuna akwai bukatar kara zage damtse kafin a akai ga gaci,” inji sanarwar.

Ya zuwa ranar Asabar, 24 ga watan Yulin 2021, sanarwar ta ce akwai cibiyoyin yin rijistar akalla 5,500 a ciki da wajen Najeriya kuma hakan zai dada saukaka aikin rijistar.

Daga nan sai suka bukaci ’yan Najeriya da su yi amfani da damar wajen kaucewa rufe musu layuka yayin karewar wa’adin.

Ta kuma ce, “Hada lambar NIN da layukan waya zai kuma taimaka wa jami’an tsaro su aiwatar da ayyukansu tare da hadin gwiwar hukumomi da bangarorin gwamnati da ke karkashin Ma’aikatar Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani kamar yadda ake bukata.”

Yanzu haka dai gwamnatin ta ce akwai akalla mutum miliyan 59.8 da suka riga suka hada lambobin da layukansu, yayin da yawancinsu suke da tsaka-tsakin layuka uku zuwa hudu.

Har ila yau, sanarwar ta ambato Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dokta Isa Ali Pantami yana yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da wasu Jihohin saboda mayar da mallakar lambar ta NIN wajibi ga dalibai.