✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba Gida-Gida ya yi alhinin mutuwar mahaifin Kwankwaso

Dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar PDP a babban zaben kasa na 2019, Injiya Abba Kabiru Yusuf, ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar, Sanata…

Dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar PDP a babban zaben kasa na 2019, Injiya Abba Kabiru Yusuf, ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa, Majidadin Kano, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.

A wata sanarwa wacce shi da kansa ya sanya wa hannu, Abba ya bayyana Marigayi Majidadin Kano a matsayin mutum mai kyawawan halaye da dabi’u ababen koyi wanda ya shafe rayuwarsa wajen hidimtawa al’umma.

Abba wanda ya fi shahara da sunan Abba Gida-Gida, ya ce, “Innalillahi Wa Inna Ilaihirraji’un, na tsinci kaina cikin dimuwa da tashin hankali a yayin da na samu labarin rasuwar mahaifin namu.”

“Saboda haka cike da alhini ina mika ta’aziyyata ga mai gidanmu, kuma jagoranma, Sanata Rabi’u Kwankwaso, danginsa da kuma al’ummar jihar Kano baki daya.”

“Ina kuma kira ga dukkanin mutanen da ke cikin juyayi na wannan babban rashi, a kan kada su manta da ka’idodin dakile yaduwar cutar Coronavirus wajen halartar jana’iza da kuma zaman makoki da za a yi wa mamacin.”

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikan marigayi Majidadin Kano kuma Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.

Aminiya ta ruwaito cewa, Allah ya yi wa Mahaifin Sanata Kwankwaso rasuwa a daren ranar Juma’a, 25 ga watan Dasimba bayan ya shafe tsawon shekaru 93 a doron kasa.