✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abdussalami ga ’yan takara: Ku ja kunnen masu magana da yawunku

Ya ce duk wanda bai ji ba, shi za su zarga

Tsohon Shugaban Kasa kuma Shugaban Kwamitin Wanzar da Lafiya na Kasa (NPC) Janar Abdulsalam Abubakar mai ritaya, ya yi kira ga ’yan takarar Shugaban Kasa da su ja kunnen masu magana da yawunsu.

Tsohon Shugaban ya fadi haka ne a wata sanarwa da ya fitar a madadin kwamitin, wanda ya kunshi wasu manyan ’yan Najeriya da suka sa hannu a ranar Litinin.

Sanarwar ta yi kira ga ’yar takarar da su da ja wa jami’an nasu kunne dangane da irin kalaman su wanda ka iya tayar da hankulan jama’a.

Ya ce kiran ya zama wajibi la’akari da rahotanin yawan fadace-fadace a yakin neman zabe da jam’iyyu ke yi tun da aka soma yakin neman zabe.

Sannan ya ce, ’yan kwamitin wanzar da zaman lafiyar sun lura da lalacewar yanayin sadarwa ta fuskar kalamai tsakanin ’yan siyasa da kuma mabiya tun da aka dage takunkumin yakin neman zabe ya karu.

“Muna kira da babbar murya ga ’yan takarar da ke neman kujerar Shugabancin Kasa da su taka musu birki a irin kalamansu a kafofin yada labarai.

“Domin za mu dora alhakin duk abin da ya biyo baya a kan dan takarar da kuma jam’iyyarsa,” inji Abdussalam.

Sanarwar dai na dauke ne da sa hannun Rabaran Mathew Hassan Kukah da Mista Attah Barkindo