✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aminiya a kauyen su Shekau: Tun yana yaro fitinanne ne —Dagaci

Aminiya ta ziyarci mahaifar Shekau, babban jigo a ayyukan ta’addancin Boko Haram.

  • Ban ga amfanin rayuwarsa ba – Mahaifiyarsa
  • Babu abin da ya jawo mana sai bakin jini – Baffansa
  • Mutuwarsa abin farin ciki ne gare mu – Abokinsa

Bayan samun labarin mutuwar Abubakar Shekau, jaridar Aminiya ta ziyarci mahaifar Shugaban Kungiyar Boko Haram din wanda ya kasance babban jigo a ayyukan ta’addanci da rashin tausayi da hallaka jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba, wadanda kiyasi ya nuna cewa ’yan Boko Haram sun hallaka akalla mutum dubu 200, baya ga raba miliyoyi da muhallinsu.

Kauyen Shekau da ke Karamar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe yana da nisan kilomita 75 daga garin Damaturu, sannan garin Babbangida ne hedkwatar karamar hukumar.

Daga Babbangida zuwa kauyen Shekau tafiya ce da ba ta fi kilomita 50 ba, amma rashin kyan hanya kan sa a shafe kusan awa daya kafin a isa kauyen Shekau.

Kauyen Shekau yana da abubuwa more rayuwa irin su wutar lantarki da ruwan sha da asibiti da makarantar boko.

Garin yana kunshe da kabilu hudu da suka hada da Bare-bari (Kanuri) da Fulani da Mangawa da sauransu, sai dai matsala daya da jama’ar garin suke fama da ita, ita ce ta rashin hanya.

Yadda Abubakar Shekau ya taso da fitina — Dagaci

Bayan da wakilin Aminiya ya isa kauyen Shekau ya fara gabatar da kansa ga Dagacin garin, Malam Lawan Gana, inda suka tattauna a kan wane ne Abubakar Shekau.

Malam Lawan ya ce hakika Abubakar Shekau dansu ne, kuma a wannan kauye aka haife shi, kuma an haife shi a lokacin mulkin soja lokacin Janar Murtala Mohammed yana Shugaban Kasa.

Ya ce kuma shi aminin mahaifin Shekau ne.

Ya ce Abor kamar yadda suke kiran Shekau, yaro ne da tun yana karami ba ya jin magana, amma yana son karatun addini.

Dagacin ya ce “Ganin hazakarsa ce ya sa mahaifinsa Malam Muhammadu wanda nakasasshe ne ya kawo shi nan gabana ya ce min’ Ba Lawan, ina son zan kai Abor karatun allo, amma ina ya kamata in tura shi?’

“Lokacin Abor bai fi shekara bakwai zuwa takwas ba don ganin yadda yake sai na ce da mahaifinsa bari a kai shi wani kauye nan kusa da namu mai suna Jumbam.

“Kuma haka aka yi a ranar da za a kai Abor kauyen Jumbam dan uwan mahaifinsa ne, ya kai shi wajen wani malami mai suna Malam Kachalla.”

Ya kara da cewa “A can ya zauna kusan shekara biyu, sai mahaifinsa ya ce min Abor ya koma Benisheik don ya ci gaba da karatunsa na Alkur’ani.

“To daga nan Benisheik ko ya yi shekara daya ne, sai ya wuce Maiduguri, yana da shekara 11 ko 12.

“Tunda aka kai Abor karatu a Jumbam har ya koma Maiduguri bai taba zuwa garin nan ba, sai bayan shekara 10 da wani abu da suka zo da Muhammad Yusuf wai sun zo yi mana wa’azi.

“Amma kafin nan mahaifinsa ya zo nan wajena, yana yi min korafi a kan halin da Abubakar Shekau ya sa kansa a ciki na shiga wata kungiyar addini.

“Ya ce min Ba Lawal ko Naira daya ce ta zo ta hannun Abor aka ba ni ban yafe ba.

“Haka har Allah Ya yi wa mahaifin nasa rasuwa, amma Abor bai leko garin nan ba. Kamar yadda na fada muku a baya sun zo wai za su yi mana wa’azi.”

Lawan Gana ya kara da cewa “Bai yi mamaki ba domin sanin halin Abor, yaro ne da yake da fitina domin babban dalilin da ya sa mahaifinsa ma ya yanke shawarar kai shi makarantar allo shi ne yawan rigima da sauran yara da yadda yake dukansu, ga shi karami amma yana da zuciya.

“Saboda haka tun lokacin da muka fara ganin halin da ya sa kansa a ciki, muka kame kanmu daga gare shi, domin ko a nan ya taba barazanar zai hallaka wan mahaifinsa, saboda ya ce abin da yake yi ba Musulunci ba ne.”

“Maganar gaskiya mun ga tasku a nan garin domin kusan a kullum sai jami’an tsaro sun zo nemansa ko ya shigo.

“Akwai ranar da sojoji suka zo suka tara dukkan matasan kauyen kan wai suna da alaka da Boko Haram.

“Ni na ce babu ko daya da a garin nan yake da ra’ayin bin sahunsa, domin muna da ilimi daidai gwargwado.

“Haka na ce musu kuma a haka suka tafi, domin duk binciken da suka gudanar ba a taba samun ko mutum daya ba da wani makami,” inji shi.

Ban ga amfanin rayuwarsa ba — Mahaifiyarsa

Mahaifiyar Shekau Falmata Modu a zantawarta da Aminiya a cikin harshen Barbarci (Kanuri) ta ce, “Ni ban san dadinsa ba, sam ban ga iyalansa ba, babu abin da zan ce ko ya mutu ko bai mutu ba, duk daya ne a wajena, domin babu wani amfani da ya yi min a rayuwa, wannan kuma sai a Lahira.

Falmata Modu, mahaifiyar Abubakar Shekau
Falmata Modu, mahaifiyar Abubakar Shekau

Amma dai hakika tana son danta domin duk uwa tana son danta ko me ya zama, sai dai ta yi Allah wadai da halin da ya shiga.

Shi ne danta na farko, amma dai ta ce ba za ta ce ta ji dadin danta ba, domin ta shafe fiye da shekara 15 ba ta sa shi a idonta ba.

Don haka ita a gare ta mutuwarsa ta fi mata.

“Ban san iyalansa balle in ga ’ya’yansa, amma dai idan suna nan Allah Ya raya su, sai dai gaskiya ina takaicin kasancewa uwa ga dan da ya jefa dubban jama’a a cikin damuwa,” inji Falmata.

Babu abin da Abubakar ya jawo mana sai bakin jini – Baffansa

Zannah Sule wanda ya ce shi yayan mahaifin Shekau ne, ya shaida wa Aminiya cewa, duk da cewa babu wani abu ko hari da aka taba kawo wa kauyen nasu sai dai a kullum ba su da sukuni, “Domin hatta ’ya’yanmu ma’aikata da suke amfani da sunan wannan gari, duk sun canja gudun kada a ce musu ’yan Boko Haram ne.

“Akwai lokacin da daya daga cikin almajiransa ya nemi hallaka ni, don na yi fito-na-fito da wannan yaro.

“Domin ka ga mu ba jahilai ba ne, muna da ilimi mun san addini don haka babu ta yadda za ka zo mana da wani sabon abu mu amince da shi.

“Ya ce mu kafirai ne, mun yi karatu ni na san cewa komai da yadda Musulunci ya tsara abinsa saboda haka babu ta yadda za ka zo mana da wani sabon abu mu karba,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Mu hudu ne muke sukan da’awarsa, da ni da Kansila Kolo da Abacha da kuma mahaifinsa.

“Mukan ce masa wannan abin da yake yi ba daidai ba ne amma ya ki ji, yanzu ga abin da ya faru da shi.”

Game da yadda garin Shekau ya yi suna, Zannah Sule ya ce, “Ai da sunan abin kirki ne ya yi, za mu yi alfahari da hakan, amma na gaya maka ko ma’aikata kai kowane mutum ba ya yarda ya ce shi daga garin Shekau yake, har ta kai mun boye sunan garin muna cewa garin Tsakiya, don haka babu wani abu da Abor ya jawo mana illa bakin jini da tsoron bayyana kanmu a tsakanin al’umma.”

Mutuwarsa abin farin ciki ne gare mu — Abokinsa

Wani da bai yarda a bayyana sunansa ba, ya ce hakika Abubakar Shekau amininsa ne tun suna yara, amma bayan tafiyarsa karatun allo suka rabu, duk da cewa lokacin da ya zo ya so ya bi shi.

“Kuma a gaskiya na so hakan amma iyayena suka hana, domin a lokacin ban fahimci manufarsa ba, na dauka wani abu ne mai kyau, suke kai, Allah dai Ya tarfa wa garina nono ban fada tarkonsa ba,” inji shi.

Ya kara da cewa “A kullum idan na je gai da mahaifiyarsa, tana kuka da nuna bakin cikinta a kan halin da Abor ya shiga.

“Takan ce kai ga iyalanka da ’ya’yanka, amma ni ka ga ban san kowa nasa ba.

“Gaskiya mutuwarsa ta kasance abin farin ciki a gare mu, domin kusan kowane lokaci garin nan yana tare da jam’ian tsaro na sirri, duk da cewa ba su taba kama kowa ba, sai dai ba mu da kwanciyar hankali.”

Abubakar Shekau ya mutu ne, bayan takaddamar da aka ce ta barke a tsakaninsa da bangaren ISWAP, wadanda suka nemi ya yi musu mubaya’a, amma ya ki, wanda hakan ya zama sanadiyar da ya hallaka kansa, inda aka ce ya tarwatsa kansa da bam da ya daura a jikinsa.

Mutuwar Abubakar Shekau ta kasance wani abu da mutane suka yi ta tofa albarkacin bakinsu, wadansu na cewa dama haka irin karshensu yake kasancewa na yin mummunan karshe.