✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta fara biyan ’yan ga-ruwa da direbobi tallafi

Tallafin shiri ne rage wa masu kananan sana'o'i radadin annobar COVID-19

Gwamnatin Tarayya ta fara biyan tallafin N30,000 ga direbobi da ’yan ga-ruwa masu tura kura.

Kakakin Mataimakin Shugaban Kasa, Laolu Akande ya ce tallafin na daga cikin shirin gwamnati na taimaka wa kananan sana’o’i domin rage radadin annobar COVID-19

Ya ce tallafin daban ne da wanda gwamnati ta kaddamar na masu sana’o’in hannu a ranar 1 ga watan Oktoba, 2020.

“Masu sana’o’in hannu da aka tantance sun fara karbar N30,000, wannan kuma matuka da masu tura kura da sauransu ne za su amfana.

“Tallafin sana’o’in hannun kashi uku ne, zuwa ranar 29 ga Nuwamba, 2020 mutum 59,000 sun amfana a jihohi 24 da ke cikin rukunin farko da na biyu.

“Jihohin su ne Abuja, Legas, Ekiti, Kaduna, Borno, Kano, Bauchi, Anambra, Abia, Ribas, Filato, Delta, Taraba, Adamawa, Bayelsa, Edo, Ogun, Ondo, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Enugu da Ebonyi.

“Ana kuma tantance rukuni na uku a jihohin Akwa-Ibom, Kuros Riba, Zamfara, Yobe, Sokoto, Nasarawa, Niger, Imo, Oyo, Osun, Jigawa, Gombe da Binuwai.

“Tuni kuma aka fara biyan masu kananan masana’auntu a bangaren ilimi, shakatawa, da sauransu tallafi.

“Shi kuma tsari mutum 500,000 ne za su amfana inda kowannensu zai samu N50,000 na tsawon wata uku farawa daga watan Oktoba; kuma tn ranar 17 ga watan Nuwamba, 2020 aka fara biyan wadanda suka samu.

“Kawo yanzu mutum 207,319 masu sana’o’i 35,837 a fadin Najeriya sun riga sun karbi na watan farko”, inji shi.