✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da Bellingham wasanni biyu a La Liga

Bellingham zai iya buga wasan da za su yi da RB Leipzig a Gasar Zakarun Turai a wannan Larabar.

An dakatar da ɗan wasan Real Madrid Jude Bellingham daga buga wasanni biyu a gasar La Liga ta Sifaniya.

An dauki mataki ne saboda jan katin da ɗan wasan na ƙasar Ingila ya karɓa a wasan da Real ta yi 2-2 da Valencia a ranar Asabar.

Tun farko Bellingham, mai shekaru 20, ya yi tunanin ya zura ƙwallo a minti na shida na ƙarin lokaci kafin a tashi daga wasan da aka buga a filin wasa na Mestalla.

Sai dai alƙalin wasa Gil Manzano ya busa tashi kafin ƙwallon ta shiga da’ira ta 18, lamarin da ya fusata ɗan wasan ya riƙa tayar da jijiyar wuya da furta kalmomi marasa daɗi saboda ganin cewa an yi alƙalanci da rashin gaskiya

A cewar Hukumar Kwallon Kafa ta Sifaniya (RFEF), Bellingham ya nuna “raini ko rashin ɗa’a ” ga Manzano lokacin da ’yan wasan Real da ma’aikatansu suka kewaye shi.

Bellingham, wanda ke dawowa bayan shafe makonni uku yana jinya, zai kuma biya tarar Yuro 600.

Real ta ɗaukaka ƙara kan jan katin da aka bai wa Bellingham, amma kwamitin ladabtarwa na RFEF ya yi watsi da hujjar cewa alƙalin wasan ya yi kuskure.

Da wannan hukuncin, Bellingham zai dawo gasar La Liga a wasan da Real Madrid za ta fafata da Athletic Bilbao a ranar 31 ga Maris bayan hutun wasannin ƙasa da ƙasa.

Amma kuma ɗan wasan zai iya buga wasan da Real za ta yi da RB Leipzig a Gasar Kofin Zakarun Turai a wannan Larabar.