✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk kuri’ar da ba ta da tambari jabu ce —Jami’an zaben APC

An fara tantance kuri'un zaben da aka yi lattin kusan awa bakwai kafin a fara

Jami’an zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC sun ce duk takardar kada kuri’a da ba ta dauke da tambari na musamman ta jabu ce.

Sun sanar da haka ne dab da fara tantance kuri’un da daliget suka kada a zaben, inda suka bayyana cewa kowace takardar kuri’a da aka yi amfani da ita a zaben ta na dauke da wani tambari na musamman, don haka duk kuri’ar da aka gano ba ta dauke da shi to ta zaba ta jabu, za a jefar.

Sun kara da cewa duk kuri’ar da aka dauko za a bude ta a nuna wa wakilan ’yan takara su gani kafin a mika ta ga wakilin dan takarar da sunansa ke jikin kuri’ar.

A halin yanzu an fara tantance kuri’un da daliget sama da 2,000 suka kada a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

An fara tantance kuri’un ne bayan kammala jefa kuri’a da misalin karfe 8 na safiyar Laraba, bayan an yi lattin kusan awa bakwai da farawa.

Mutum 14 ne dai suka fatata za zaben fidda gwanin, wanda ya yi nasara a cikinsu, shi ne dan takarar shugaban kasar jam’iyyar mai mulki a zaben 2023.

Wannan na zuwa ne dai bayan dambarwar zabo dan takara ta hanyar maslaha ta gagara a jam’iyyar.